Tarayyar Turai za ta zuba jarin biliyoyi a Afirka ta Kudu
March 14, 2025Talla
Galibin ayyukan da kudaden za su taimaka wa dai, su ne fannonin makamashi da ba su da lahani ga muhalli musamman na Solar da kuma wadanda ke amfani da iska.
Haka ma bisa tsari, biliyoyin na dalolin za su shafi ayyukan sarrafa magungunan rigakafi.
Kasar Afirka ta Kudun dai ita ce kan gaba a bangaren ci gaban tattalin arziki a Afirka, kuma babbar abokiyar huldar Tarayyar Turai a yankunan bakar fata.
Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa ya ce matakin ya zo ne a lokacin da tattalin arzikin kasar ke bukatar hakan, yana mai alakanta tasirin matakan tattalin arziki da shugaban Amurka Donald Trump da suka shafi kasar.