Tarayyar Turai ta yi kiran a tsagaita wuta a Zirin Gaza
June 27, 2025Jagororin kungiyar Tarayyar Turai sun bukaci a dakatar da bude wuta nan take a Zirin Gaza tare da yin kira ga Isra'ila da ta tabbatar da mutunta dokokin jinkai.
Haka ma shugabannin sun kuma bukaci Isra'ilar ta janye shingen da ta kafa a Gazar domin samun saukin isar da kayan agajin ba tare da wata matsala ba.
Jagororin sun fitar da wannan sanarwa ne a taron Majalisar Turai da aka gudanar a Brussels.
A makon da ya gabata, shashen diflomasiyya ta EU ta bayyana cewa akwai alamun Isra'ila ta karya ka'idojin hakkin dan Adam da aka shimfida a yarjejeniyar da ke tsara dangantakarta da EU.
A lokaci guda, shugaban kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya yi kira ga Majalisar Turai da ta aika da sako mai karfi cewa tana goyon bayan kokarin kasarsa na shiga Tarayyar Turai.
Shugaban Ukraine ya maimaita bukatarsa ta kakaba wa kudaden man fetur na Rasha takunkumi da ma kara takunkumai kan kasar.