Tarayyar Turai ta bai wa Najeriya kudaden tallafa wa talaka
March 13, 2025Jihohin da za su ci gajiyar tallafin kudi Euro miliyan 46 din dai sun hada ne da Abia da Sokoto da Oyo da kuma Binuwai, inda asusun kula da lafiyar yara kanana na Majalisar Dinkin Duniya ya kaddamar da shirin a Abuja.
Kaddamar da wannan sabon shiri ya nuna hada kan da wadannan hukumomin suka yi domin fadada tsarin samar da tallafi ga marasa galihu a Najeriya, wadanda a yanzu daukacin su kashi 14.8 na al'umar kasar ke cin gajiyar wannan tsari, duk da dumbin mutanen da ke fuskantar kuncin talauci a Najeriyar musamman mata da yara kanana da majalisar dikin duniyar ta bayyana kaso 70 suna zaune a yankunan karkara.
Kungiyar Tarayyar Turai ita ta samar da tallafin, da gwamnatin kasar Jamus ne suka hadu suka samar da kaso mai tsoka na Euro milyan 46 don wannan aiki da aka kaddamar a Abuja.
Muhimmin aikin da za a yi a yanzu, shi ne fadada rajistar masu bukata a jihohin Abia da Sokoto da Oyo da kuma jihar Binuwai domin tabbatar da sahihancin rajistar bisa ga cancanta da kawar da cusa siyasa a tsarin.
A shekarun baya dai an fuskanci matsaloli inda mutanen da aka sanya sunansu a rijistar akan yi masu kwange na hakkokinsu.
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya samar da fiye da dala milyan 13 bisa manufar kyautata rajistar tsarin tallafa wa marasa galihu da aka yi wa lakabi da Susi a Najeriyar. Tallafin da aka bayar na fatan Najeriya ta kyautata tsarin ta yadda za a rage matsalar talauci a tsakanin alumma.
Najeriyar dai na da sauran aiki a gaba wajen kyutatawa da inganta tsarin tallafa wa marasa galihu a cikin kasar wanda yake cike da matsaloli.