Talla na hana wasu yaran mata zuwa makaranta a Najeriya: WB
January 30, 2025Azima da Aisha, wasu 'yan mata ne da ke da shekaru 10 zuwa 13 da haihuwa da ke kauyen Jere da ke wajen babban birnin tarayya na Abuja, kuma suna talla maimakon kasancewa cikin aji kamar ragowar yara. Labarin yaran matan guda biyu na zaman halin da miliyoyin 'yan mata ke ciki a daukacin tarayyar Najeriya, kasar da ke kallon karuwar yara da ba su da daman yin karatu a yanzu haka.
Karin bayani: Kalubalen ilimin mata 'yan gudun hijira a duniya
Wani rahoton Bbankin Duniya ya ce kaso 66% na yan matan da ke kasar dai ba a ba su damar kaiwa zuwa matakin karamar sakandare cikin kasar ba. Najeriya ta ciri tutar zama ta kan gaba a duniya baki daya wajen koma bayan karatun 'yan mata a duniya baki daya.
Karin bayani: Nijar:Tsarin inganta ilimin yara mata
Duk da cewar kasar ta rattaba hannu kan yarjejeniyoyi na kare 'yancin yara, amma a zahirin rayuwa da,i miliyoyin yara a kasar ba su da damar karatun duk da ikirari na gwamnatoci a jihohin kasar daban-daban.
Akalla 'yan mata miliyan kusan takwas ne ba sa zuwa makaranta a cikin tarayyar Najeriya. Shi Kansa Banki Duniya na jagorantar wani sabon shiri na sake komawar 'yan matan zuwa aji. Sai dai a tunanin Abdul Aziz Abdul Aziz da ke bai wa shugaban kasar shawara kan harkokin labarai, komawa zuwa ajin zai yi nasara ne da hadin kai na iyayen yara a ko’ina. Talauci na sa miliyoyin 'yan mata komawa talla, game da auren wuri da ke sa kaso 35% na 'yan matan shiga cikin barazanar mai girma