Afghanistan: Shekaru hudu da mulkin Taliban
August 15, 2025Gwamnatin 'yan Taliban na bikin cika shekaru hudu da dawowa kan karagar mulkin Afghanistan, tare da dukan kirji da matakin Rasha na kasancewa kasa ta farko da ta amince da su a matsayin halastattun hukumomi.
Karin bayani: Rasha ta amince da daular Musulumci Taliban a hukumance
Rahotanni da ke fitowa daga kasar na cewa tun da yammacin jiya Alhamis ne aka fara gudanar da shagulgula, inda 'yan Taliban suka taru a wata mahadar hanya da ke zuwa ofishin jakadancin Amurka suna wasan wuta tare da daga manyan tutoci.
A wannan rana ta Juma'a an shirya fareti a wasu biranen kasar ciki har da Kabul fadar gwamnati, sai dai mahukuntan na Taliban sun ce sun soke faretin da bisa ala'ada ake yi a barikin soji na Bagram inda suka yi dauki ba dadi da sojojin Kasashen Yamma daga 2001 zuwa 2021 a lokacin da aka yi kokarin murkushe su.
Bikin na zuwa ne dai a daidai lokacin da kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa ke ci gaba da mayar da gwamnatin Taliban saniyar ware tare da kin amincewa da halascinta saboda tsauraran dokokin da ta shinfida.