Najeriya: Takaita motocin dakon mai a kan tituna
February 20, 2025Sau dai dai har kusan 28 ne dai manyan tankoki na dakon man fetur suka kai ga faduwa cikin tsawon kasa da shekaru biyu a tarayyar Najeriya.
Sama da mutane 98 ne dai alal ga misali suka rasu a kauyen Dikko da ke can a jihar Niger cikin watan Janairun da ya shude, kuma kafin nan dai tarayyar Najeriyar ta yi asarar 150 daga hatsarin tankar dakon man fetur a watan Oktoban bara a Majiya da ke a Jigawa.
To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce ta takaita amfani da manyan tankunan dakon man fetur hawa a titunan kasar tun daga ranar daya ga watan gobe na Maris. Hukumar kula da harkokin man fetur a Najeriya dai ta ce, duk wata tankar da ke iya daukar lita 60,000 ta hajjar man fetur, to ba a yarda ta hau tituna cikin sunan dakon hajjar ba.
Ya zuwa zangon karshe na shekarar bana dai, hukumar ta ce tankokin dako da basu wuci daukar lita 45,000 ne kadai ke da ikon hawa a titunan da sunan daukar hajjar mai tasiri. Najeriyar dai ta dauki lokaci cikin al'adar dakon man fetur ta tankuna daga sashen kudanci zuwa a arewacin kasar.
Sama da motoci 2,000 ne dai haramcin ke iya shafa a daukacin tarayyar Najeriya, abun kuma da ke shirin jawo asarar da ta kai kusan Naira miliyan dubu 300 a bangaren masu kasuwar.To sai dai kuma a yayin da gwamnatin ke shirin rushe tsohon tsarin dake zaman al'ada babu alamun wani sabon dake shirin maye masa.
Rushewar bututu na dakon tatattacen man fetur cikin kasar dai ya sanya kusan kaso 80 cikin 100 na man fetur din tarayyar Najeriyar na hawa na tituna ne daga sashen kudu zuwa arewacin kasar domin amfani.
Abubakar Ali dai na zaman kwarrare ga tattali na arzikin kasar kuma ya ce kasar bata da zabi face sake farfado da layin dogo. Sama da tankuna dubu biyar ne dai yanzu haka ke kara kaina domin cika buri na yan kasar cikin hajjar man. Najeriya dai yanzu haka na shan abun da ya kai lita man miliyan 50 kullum.