SiyasaJamus
Kasar Rasha ta gayyaci jakadan Jamus da ke a birnin Moscow
June 27, 2025Talla
Jakadin na Jamus a Rasha Alexander Graf Lambsdorff, an gayyace shi zuwa ofishin ministan harkokin waje na Rasha don yin bayyani.
A farkon watan Yuni Jamus ta ki amincewa da tsawaita takardar izinin zama ta Sergei Feoktistov, shugaban ofishin labarai mallakar gwamnatin kasar Rasha a Berlin.
Sannan ta umarceshi da ya fice daga kasar nan da ranar 19 ga watan Agusta.Tashe-tashen hankula tsakanin Moscow da kasashen yammacin duniya:
Musamman Jamus, abokiyar kawance Ukraine wadda take bai wa makamai na ci gaba da yin kamari tun bayan farmakin da Rasha ta kai wa Ukraine a watan Fabrairun na shekara ta 2022.: