Kai ruwa rana a kan dokar zabe a Njeriya
March 21, 2022Dagar da ‘yan majalisar suka yi tare da hawa kujerar na ki a kan bukatar shugaban Najeriyar na su cire wannan sashi na 84 sakin layi na 12 na dokar zaben Najeriyar ne ya sanya ministan shari’a kuma attorney janar na Najeriya ya bayyana daukan wannan mataki na cire wannan sashi daga dokar zaben Najeriyar ta 2022, bayan da wata kotu ta bayyana cewar sashin dokar ya ci karo da ‘yancin ‘yan Najeriya na tsayawa takara. Wanan sashi na doka dai ya bukaci masu rike da mukaman siyasa su sauka daga mukammansu ana saura watani shida a yi zabe. To sai dai tuni ‘yan majalisar suka bayyana cewar mataki na goge wannan sashi da ministan shari’ar ya ambata ba zata sabu ba, domin kamata ya yi a duba abin da kotu ta bayyana shari’ar da ta yanke. Sanata Ahmed Baba Kaita dan majalisar datawan Najeriyar ne: ''Wannan sashi na 84 saki layi na 12 na dokar zaben Najeriyar dai ya haifar da kace-nace a tsakanin masu rike da mukamman siyasa. Shin minsitan shari’a na da ikon goge wani sashi na doka da ‘yan majalisa suka yi? Barrister Buhari Yusuf lauya ne mai zaman kansa a Abuja. Da alamun za’a ci gaba da ja a kan wannan batu har zuwa kotun kolin Najeriya wacce daga ita sai dai a hakuri bisa hukunci da za ta yanke sanin yadda ‘yan majalisar suka ja da ya kai ga bijirewa bukata shugaban Najeriyar a kan su cire wannan sashin na 84 daga dokar zaben amma suka tirje.