SiyasaTaiwan
Taiwan na bukatar zaman lafiya da China
May 20, 2025Talla
Shugaban Taiwan Lai Ching-te ya ce kasarsa a shirye ta ke ta tattauna zaman lafiya da China, to amma za ta ci gaba da daukar matakin karfafa tsaronta ko da Beijin za ta nemi tursasa ikrarinta na mallakar tsibirin da karfin soji.
Kalaman na Lai na zuwa ne yayin da ya cika shekara guda a karagar mulki.
A baya dai China ta baiyana shi a matsayin dan aware bayan da ya yi watsi da tayin tattaunawa.
A 'yan shekarun baya China ta tsananta atisayen soji a kusa da Taiwan a wani mataki da ake yi wa kallo na tsokanar fada.