Kasashen duniya na taimakon Najeriya kan tsaro
August 19, 2022Wannan dai wata sabuwar dubara ce da gwamnatin Najeriya ta bullo da ita a tsari na gwama amfani da karfin bindiga da kuma laluma da tuntubar juna, don shawo kan matsalar rashin tsaro da ta adabi al'ummar, musamman ayyukan ta'adanci da na ‘yan bindiga da ke daji.
Karin Byani:Fargaba a zukatan 'yan Najeriya
An dai tabo batun samar da ‘yan sandan al'umma ko kuwa na jihohi a matsayin mafita daga matsalar don su shiga cikin al'umma. Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS dai ta bayyana goyon baya da ma taimakon da za ta bayar a wannan aiki, sanin cewa matsalaoli na rashin tsaro sun watsu zuwa kasashen da ke makwabtaka da Najeriya.
Ita kanta kungiyar tarayyar Turai ta EU, ta bi sahu a wannan sabon kokari da Najeriya ke yi tare da alkawarin ba da taimako kamar yadda Jerome Reviere ya bayyana. Matsalar rashin tsaro dai ta haifar da koma baya a Najeriya tare da tilasta dakatar da ayyukan ci-gaba da suka kai Naira tirliyan 12 a shekara ta 2021.