Tabarbarewar jinkai a gabashin Kwango
February 3, 2025Rikicin da ke wakana a gabashin kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango dai na ci gaba da yin barazana ga al'umma da kuma yunkuri wajen durkusar da fannin kiwon lafiya saboda karuwar da ake samu ta wadanda aka jikkata musamman ma a birnin Goma inda 'yan tawayen M23 ke ta kokarin karbe shi da karfin tuwo.
Karin Bayani: DR Kwango ta tabbatar da kasancewar sojojin Ruwanda a Goma
Masu sanya idanu kan rikicin sun ce yanzu haka asibitocin da ke Goma sun cika makil da marasa lafiya wanda suka jikkata sakamakon rikicin kuma jami'an kiwon lafiyar na gab da gaza kula da su saboda karuwar da suke yi cikin hanzari. Emmanuel Kone da ke aiki da Kungiyar Red Cross a Goma din ya ce a 'yan kwanakin da suka gabata sun ga tururuwar mutane da suka jikkata ciki kuwa har da mata da kananan yara.
Yayin da bangaren kiwon lafiya ke ci gaba da fuskantar barazanar durkushe a Goma saboda adadin wadanda suka jikkata, mazauna sauran yankunan da ke makwabta da Goma din ciki kuwa har da Bukavu sun ce hankalinsu a tashe yake inda wasunsu suka fara kauracewa gidanjensu yayin da suka fara shiga kasuwanni don sayen kayan masarufi don zama cikin shirin ko-ta-kwana.
A daura da wannan fargaba da mutanen Bukavu ke fama ita da irin halin da al'umma suka tsincin kansu a ciki a Goma, musamman ma batu na kalubale ta fannin kiwon lafiya da kuma durkushewar ababan more rayuwa, kasashen Afirka ciki kuwa har da Afirka ta Kudu sun ce za su ci gaba da yin bakin kokarinsu wajen ganin zaman lafiya ya wanzu a gabashin Kongo din.
Ita ma dai Ruwanda wadda ake kallo a matsayin kanwa uwar gami kan rikicin kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango saboda zargin da ake yi mata na mara baya ga 'yan tawayen M23 ke cewar ta yi maraba da shirin da ake yi na wani zama na musamman da aka kira kan rikicin wanda zai hada kan kasashen kungiyar SADC da nufin lalubo bakin zaren warware rikicin don gudun kada ya yadu a sauran sassan kasar da ma kasashe makwabta.