Taba Ka Lashe : 27.08.2025:
September 2, 2025Talla
Jami'o'i a arewacin Najeriya da ke gudanar da aikin bincike-bincike da zakulo al'adun kasar Hausa sun dukufa wajen binciko tarihi da rayuwar makadan kasar Hausa, da suka yi zamani suka kuma shude, wannan dai ya sa Jami'ar Jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya bin sahun sauran takwarorinta jami'oi ‘wajen gudanar da irin wannan bincike-bincike.