Taƙaddamar Amirka da Rasha
May 18, 2011Shugaba Dmitry Medvedev na Rasha ya ce shirin Amirka na girke garkuwar makamai masu linzami a yankin tsakiya da gabashin Turai wani mataki ne da zai iya tilasta wa ƙasarsa janyewa daga yarjejniyar ƙayyade makaman nukiliya . A cikin jawabin da yayi ta telebijan Medvedev ya ce garkuwar makamai masu linzami da Amirka ke shirin girkewa abu da zai iya yin barazana kai tsaye ga ƙarfin dake gareta na makaman nukiliya, a baya ga tilasta mata yin watsi da matsayin da aka kayyade wa kasashe na harba makamai masu linzami. Medvedev ya faɗi haka ne yana mai nuni da wata aya da yarjejeniyar ƙayyade makaman nukiliya ta Start ta tanada, wadda ta bai wa Rasha ikon yin watsi da alƙawarin da ta ɗauka game da wannan yarjejeniya.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Ahmad Tijani Lawal