Super Eagles: Halin kila wa kala a share fagen kofin duniya
March 24, 2025A nahiyar Afirka, an gudanar da wasannin mako na biyar da na shida na neman tikitin buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya da kasashen Kanada da Mexiko da Amurka za su dauki bakunci. An fara barje gumi tun daga ranar 19 ga Maris, inda aka yi ruwan kwallaye a filayen wasanni daban-daban... Wasu daga cikin wasanni da suka dauki hankali sun hada da karawa tsakanin Ghana da Chadi a rukunin I inda tawagar Black Stars ta zazzaga wa Chadi kwalaye 5 da neman, lamarin da ya bata damar jan ragamar wannan rukuni da maki 12 ,kafin ta buga wasanta na mako na shida a daren yau Litinin inda za ta kalubalanci Madagaskar...
A rukunin D, wanda tsibirin Cap Vert ke jagoranta da maki 10, Kamaru da ke a matsayi na biyu da maki 9 ta yi canjaras da Eswatini ba tare da an ci kwallo ba. Sai dai tawagar ta Lions Indomptables za ta karbi bakunci Libiya da ke a matsayi na 3 da maki 8 a gobe Talata don sauya makomarta a wannan rukuni.
A rukunin E, Jamhuriyar Nijar da ke a matsayi na biyu da maki 6 ta kusa yi wa Maroko sakiyar da babu ruwa a fafatarwar da suka yi. Hasali ma, an tafi hutun rabin lokaci Mena ta Nijar na da kwallo daya Maroko na nema, kafin al'amaru su juya a karshen wasa inda Maroko ta yi nasara 2 da 1, lamarin da ke nunar da cewa tana iya samun tikitinta tun a wasan mako na shida da za ta buga da Tanzaniya a gobe Talata. Amma ita kuwa jamhuriyar Nijar an daga karawar da za ta yi da Iritiriya zuwa gaba yayin da 'yan kasar ke cike da fatan ganin Mena ta yi abun kai.
A rukunin C, tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi abin kai inda ta doke Ruwanda a gidanta ci 2- 0, kwalayen da dan wasan gaba Viktor Osimhen ya ci tare da taimako ademola Lukuman da kuma Shukwueze. Sai da akwai jan aiki a gaban Najeriyar domin dai duk da wannan nasara tana a matsayi na 4 da maki 6, yayin da za ta kalubalanci Zimbabuwe a wasan mako na shida a gobe Talata. Wannan ne dai wasan farko da tawagar ta Super Eagles ta buga karkashin sabon mai horaswa Eric Chelle wanda aka cefano domin dawo da kimar Najeriya a fagen kwallon kafa.
Wasanni neman tikitin kusa da na karshe na Nations League
Bayan kwashe shekaru masu sarkakiya, tawagar kwallon kafa ta Jamus ta sake farfadowa inda ta yi tattaki zuwa Italiya inda ta lallasa babbar abokiyar hamayya Sqadura Azura ci 2-1 a wasan dab da na kusa kusa da na karshe na Nations League. Wannan nasara ta bai wa abokan wasan Jamal Musiala damar samun tikiten buga wasan kusa na karshe na gasar inda za su kalubalanci Potugal a ranar 04.06.2025. Tun dai bayan zuwan mai horaswa Julian Nagelsmann, tawagar ta Manschaft ta mike inda take gasawa abokan karawarta aya a bannu tare da samun kikkyawan sakamo a dukannin wasanni da take bugawa.
A nata bangaren, Spain mai rike da kofin kasashen nahiyar Turai ta kai bantenta da kyar da jibin goshi a gaban Netherland a bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan sun tashi wasa ci 3-3 a birnin Valencia. Tawagar ta Spain karkashin mai horaswa Luis De la Fuente za ta fafata da Faransa da to doke Croaitia a ranar 05.06.2025.
Tuchel ya dora Three Lions a kan kyakkyawar turba
A nan kuma, mai horaswa Thomas Tuchel ya fara jagorantar tawagar kasar Ingila ta kafar dama, inda a wasan farko da kocin dan kasar Jamus ya jargoranta ya samu nasara a kan Albaniya da ci biyu da nema a wasan neman gurbin buga gasar cin kofin duniya ta 2026. Sai da, gabanin wasan da tawagar ta Three Lions za ta buga a wannan Litinin da kasar Lutiyoniya, kocin ya ce bai gamsu dari bisa dari da bajimtar da 'yan wasansa suka nuna ba, yana mai bukatar ya ga karin azama daga wasu 'yan wasan irin Marcus Rashford da Foden.
'Yar Afirka ta zama shugabar Kwamitin Olympics na Duniya
A karon farko an zabi 'yar Afirka kuma matashiya a matsayin shugabar kwamitin Olympics na Duniya inda Kirsty Coventry 'yar kasar Zimbabuwe za ta gaji Thomas Bach dan kasar Jamus. Zaben Kirsty Coventry, 'yar wasan ninkaya wadda ta taba lashe kyauta a tseren mita 200 sau biyu a matsayin shugabar hukumar wasanni mafi mahimmanci a duniya zai karfafa gwiwa ga mata na su kara azama a fagen wasanni . Sannan, dama ce ga Afirka na cika buri a game shirya gasar wasannin Olympics watan wata rana. Sai dai jim kadan bayan zabenta, Kirsty Coventry ta ce shirya gasar wasannin Olympics ta matasa a birnin Dakar na kasar Senegal a shekarar 2026 mai zuwa zai kasance matakin farko na zakaran gwajin dafi ga nahiyar ta Afirka.