SiyasaAfirka
Sudan ta Kudu: Riek Machar na fuskantar daurin talala
March 27, 2025Talla
Dukkanin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar bukatar wanzar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu a 2018, sun bukaci warware dukkan takaddamar da ke tsakani cikin kwanciyar hankali da lumana domin ci gaban kasar ta Sudan ta Kudu da kuma kasashen da ke shiyyar.
Karin bayani:Sojojin da ke biyeyya ga Shugaba Kiir sun kama mataimakinsa Riek Machar
Sojojin gwamnati dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Mr. Machar a babban birnin Juba.
Karin bayani:Sudan ta Kudu ta kafa dokar hana fita bayan zanga-zanga
Tuni dai wasu daga cikin ofisoshin jakadancin kasashen duniya irin su Jamus da Norway suka rufe ofisoshinsu da ke birnin Juba, domin gudun rincabewar rikici.