Sudan: Sojojin gwamnati sun kara samun galaba
March 22, 2025Talla
Bayan galabar sake karbe iko da fadar shugaban kasa da sojojin na Sudan suka yi a ranar Juma'a, a wannan Asabar, dakarun gwamnatin sun yi nasarar korar mayakan RSF a cikin garin Kahrtoum inda manyan ofisoshin gwmanati ke da zama.
Mai magana da yawun sojojin Birgediya Janar Nabil Abdullah ya ce jami'ansu sun tsaurara tsaro a muhimman wuraren da suka hada da babban bankin Sudan da gidan adana kayan tarihi na kasa da sauran muhimman gine-ginen gwamnati da ke cikin kwaryar birnin Khartoum. Babban sojan ya ce a sakamakon hakan, abokan aikinsa sun yi nasarar bindige mayakan RSF masu yawa.