Sudan: RSF ta ayyana kafa gwamnatin hadin kan kasa
April 16, 2025Shekaru biyu bayan fara yakin basasar Sudan da ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, rundunar ko ta kwana ta RSF ta ayyana gwamnatinta da ke adawa da wacce sojojin kasar ke marawa baya, lamarin da ya kara dagula fargabar dara kasar gida biyu. Shugaban rundunar RSF Mohamed Hamdan Daglo ne ya yi amfani da kafar Telegram, wajen sanar da kafa gwamnatin da ya danganta da ta zaman Lafiya da hadin kan kasa, yana mai cewa kawance ne da ke wakiltar bangarori daban daban na Sudan.
Karin bayani: Fargabar rinchabewar rikicin Sudan ta Kudu
Tun a watan Fabrairu ne a kasar kenya, RSF da kawayenta suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar ta shata sabon salon tafiyar da Sudan, wanda ya tanadi sabon kundin tsarin mulki da kafa gwamnati hada gwiwa mai mambobi 15 da za su fito daga yankuna daban-daban na kasar. Amma manazarta sun yi gargadin cewa wannan yunkuri zai iya raba kan Sudan, musamman a yankin Darfur inda rundunar RSF keRikicin Sudan yana daukan hankali da tasiri sosai.
Karin bayani: Rikicin Sudan yana daukan hankali
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin na Sudan da ya fara a ranar 15 ga Afrilun 2023, a matsayin mafi munin matsalar jin kai a duniya, inda aka tilasta wa mutane miliyan 13 kaurace wa gidajensu, yayin da sama da mutane miliyan 3.5 suka tsere zuwa kasashen ketare.