Sudan na fuskantar barazanar fari
June 10, 2025Daractar hukumar WFP a kasar, Lauren Bukera ta ce hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta samu rahotannin da ke nuna yadda ake fama da tsanannin yunwa a yankin Jabal Awliya da ma wasu sansanonin 'yan gudun hijira a kusa da El Fasher. Ta ce sun kuma gano yadda ake fama da karancin ruwan sha da magunguna da wutar lantarki a wasu sassan.
Karin bayani:Yunwa na kashe yara a Sudan in ji UNICEF
Hukumar ta bukaci kasashen duniya da su dauki mataki cikin hanzari ta hanyar kara samar da kudade don dakatar da yunwa, a yankunan da aka fi fama da bala'in da kuma saka hannun jari don farfado da Sudan. A kalla mutane milliyan 25 ne suke fara da matsanancin karancin abinci a fadin kasar. Rikici tsakanin dakarun kasar da kuma mayakan RSF da ya barke a shekarar 2023, ya yi sanadin dububban mutane tare da haifar da matsalar yunwa mafi girma a duniya.