Jaridun Jamus: Sudan da rikicin Angola
August 8, 2025Hukumar Samar da Abinci ta Duniya, ta yi gargadin yunwa a wani yanki na Sudan", wannan shi ne taken labarin da jaridar Zeit Online ta wallafa a kan yakin basasar Sudan da duniya ke neman mantawa da shi. Birnin El Fasher da ke yammacin Sudan ya shafe fiye da shekara guda yana karkashin kawanyar sojojin tawaye na RSF, kuma a cewar hukumar samar da abinci ta duniya, yunwa na neman yin kaka gida a can. Babban birnin jihar Darfur ta Arewa, Al-Fasher ne babban birni daya tilo a yammacin Sudan da ba ya karkashin ikon sojojin RSF. Bayan fiye da shekaru biyu na yakin basasa, Majalisar Dinkin Duniya ta kiyasta cewa har yanzu mutane kusan dubu 300 na rayuwa a can.
"Angola ce kasa ta baya-bayan nan a Afirka da ta fuskanci tashin hankali sakamakon karin farashi da rashin daidaito da yunwa da ke karuwa a fadin kasar da janyo fushin al'umma", inji jaridar Süddeutsche Zeitung a kan rikicin baya-bayan nan da ya mamaye kasar ta Angola. An shafe kwanaki ana yajin aikin gama-gari a birnin Luanda, tare da zanga-zangar da jami'an tsaro suka yi kokarin amfani da bakin bindiga wajen dakatar da ita bayan an fara kwasar ganima. Adadin wadanda suka mutu a hukumance ya kai 30, yayin da wasu 270 kuma suka jikkata. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun bayyana damuwa kan yadda aka rika bude wuta, a kan mutanen da ba su da makami. A yayin da shugaban Angola Joao Lourenco ya yaba wa 'yan sandansa, saboda maido da doka da oda.
Jaridar die Tageszeitung ta buga sharhinta ne, a kan zaman doya da manja da ke tsakanin kasashen Afrika ta Kudu da Zambiya. Jaridar ta ce watanni biyu bayan mutuwar tsohon shugaban Zambia Edgar Lungu a Afirka ta Kudu, wata kotu a Pretoria ta yanke hukuncin a binne shi a Zambiya. Wannan batu dai, ya dagula dangantaka tsakanin kasashen biyu. Lungu wanda ya mulki Zambiya daga 2015 zuwa 2021, ya rasu ne a ranar biyar ga watan Yuni a wani asibiti a kasar Afrika ta Kudu yana da shekaru 68. Gwamnatin magajinsa, Hakainde Hichilema ta bayar da umarnin a maido da gawar gida a kuma yi makoki na kwanaki bakwai a kasa, har zuwa lokacin da za a yi masa addu'ar karramawa a hukumance a wurin jana'izar aka kebe domin shugabannin da suka rasu. Sai dai iyalan Lungu wadanda suke ganin gwamnatin Zambiya na musu bi ta da kulli, sun so a binne mamacin a Afirka ta Kudu. Wannan wani sabon babin rikici ne, wanda ba a taba ganin irinsa ba Zambiya.