Halin da ake ciki a wasannin Lig-Lig na kasashen Turai
March 31, 2025Cikin labaran wasannin namu na yau, muna dauke da sakamakon wasu wasannin lig-lig na kasashen Turai da wasu fannonin wasannin.
A bangaren Bundesliga da aka kara a Jamus:
Leverkusen 3, Bochum 1
Hoffenheim 1, Augsburg 1
Wolfsburg 0, Heidenheim 1
Mönchengladbach 1, RB Leipzig 0
Holstein Kiel 0, Bremen 3
Eintracht Frankfurt 1, Stuttgart 0
Freiburg 1, FC Union Berlin 2
Dortmund 3, Mainz 1
Kuma wasan da Bayern Munich ta doke FC St. Pauli 3 da 2 muka kawo muku kai tsaye inda Abdulrahim Hassan tare da Zaharadeen Umar Dutsen Kura suka jagoranta:
Yanzu haka kungiyar RB Leipzig da ke cikin masu kara wasannin na Bundesliga na Jamus ta sallami horas da 'yan wasan kungiyar, Marco Rose saboda rashin tabuka abin azo a gani a wasannin Bundesliga inda aka maye gurbinsa da Zsolt Low har zuwa karshe wasannin na Budesliga da ke wakana.
Aryna Sabalenka 'yar kasar Belarus wadda take gaba-gaba cikin fitattun 'yan wasan Tennis na duniya ta doke 'yar Amurka Jessica Pegula 7-5 6-2 inda ta lashe wasan Miami Open da aka yi a Florida da ke Amurka. Ita dai Sabalenka take matsayi na farko a duniya na gwanayen kwallon tennis na mata, kuma ta kasance a matsayi na biyu gasar da aka yi na Australiya Open a watan Janairu na wannan shekara ta 2025.
A hukumance Tiger Woods wanda ya fi kowa shahara a wasan kwallon lambu wato Gulf, ya tabbatar da cewa ya fara neman Vanessa Trump wadda take tsohuwar matar Donald Trump Jr., wato dan Shugaba Donald Trump na Amurka. Shi dai Wood mai shekaru 49 da haihuwa ya bukaci gani rashin kutse daga bangaren masu bin diddigi rayuwarsa. A tsaon lokacin da Tiger Wood ya kwashe yana wasan kwallon lambu ya lashe manyan wasanni 15.
Masu sauraro gaba daya da haka shirin ya kawo karshe a madadin wanda suka taimaka shirin ya zo muku da sauran abokan aiki Suleiman Babayo ke cewa a kasance lafiya daga nan Sashen Hausa na DW.
A wasannin La Ligar Spain, hamayya na kara kamari tsakanin Barcelona da Real Madrid a kan wanda zai zama zakara a kakar wasanni ta bana.
Kowannen su ya samu nasara a wasannin mako na 29 inda a Real Madrid ta casa Leganes ci 3-1 yayin da Barcelona ta yi wa Girona dukan kawo wuka ci 4-1. A yanzu Barcelona za ta ci gaba da jagorantar teburin Laligar da maki 66 yayin Madrid ke biye mata da maki 63.
Sai al'amura sun fara sukurkuce wa Atletico da Madrid da ke a matsayi na uku da maki 57 bayan ta yi canjaras 1--1 a karawarta da ta yi da Espayol da Barcelone lamarin da ya kara rata ta maki 9 tsakaninta da Barcelona de ci gaba da jan zarenta a kan teburin Laliga ta bana.
A wasannin lig na La Liga da aka kara a Sifaniya, kungiyar Barcelona ta raga-raga da Girona 4 da 1, kungiyoyin biyu sun kasance masu hamayya da juna domin duk suna yankin Kataloniya na Sifaniya.
Real Madrid ta doke Leganes 3 da 2, Espanyol da Atletico Madrid sun tashi 1 da 1, yayin da Villarreal ta bi Getafe har gida ta lalla ta 2 da 1.