SPD za ta tsai da shawara kan hadaka da CDU a Jamus
April 30, 2025A ranar Laraba ne 'ya'yan jam'iyyar SPD a Jamus za su tsayar da shawara kan yin hadaka da jam'iyyar CDU/CSU mai rinjaye a Majalisar Dokokin kasar ko kuma a a.
Idan suka amince da yin hadakar, wannan ne zai kai ga kafa sabuwar gwamnati a kasar ta Jamus mafi karfin tattalin arziki a Turai.
Jam'iyyar CDU ta gabatar da jerin ministocinta a sabuwar gwamnati
Yin hadakar ita ce kadai mafita ga samar da sabuwar gwamnati bayan dukkan jam'iyyun sun samu koma baya a zaben da ya gabata a watan Fabrairu.
Dukkan jam'iyyun biyu sun yi watsi da yin hadaka da jam'iyyar AfD mai kyamar baki wacce ta kasance ta biyu mafi rinjaye a majalisar dokokin Jamus ta Bundestag.
CDU ta cimma yarjejeniyar kafa sabuwar gwamnati a Jamus
Jagoran jam'iyyar CDU/CSU Friedrich Merz ne ake sa ran zai zama sabon Shugaban Gwamnatin Jamus idan hadakar ta cimma nasara.