Spain ta gano dalilin katsewar lantarki da aka fama da ita
June 17, 2025A kasar Spain, an samu karin bayani a game da babbar matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru a ranar 28 ga Afrilun da ya gabata.
Idan za a tuna dai, dukkanin fadin kasar tare da makwabciyarta Portugal ne suka fuskanci matsalar daukewar wutar lantarkin, inda zirga-zirgar jiragen kasa suka tsaya, an kuma soke tafiye-tafiyen jiragen sama, sannan fitilun kann hanya ma duk suka daina aiki.
Wani rahoto da gwamnatin Spain ta fitar a yau ya nuna cewa, kamfanonin samar da wutar lantarki da wasu kamfanonin ne ake zargi.
An yi zargin cewa karuwar karfin wutar lantarki ne ya haifar da jerin matsaloli a hanyoyin samar da makamashin.
Wasu kamfanoni sun yanke shawarar kashe na'urorinsu don kare kayan aikinsu, wanda hakan ya jawo karin katsewar wuta a wasu wurare, har ta kai ga yaduwar matsalar.