Spain ta bukaci daukar matakin ladabtar da Isra'ila
May 25, 2025Taron da zai sami halartar kasashen 20 da kungiyoyi masu zaman kansu zai mayar da hankali ne kacokam a kan bukatar kawo karshen yakin in ji minista Jose Manuel Albares.
Ministan a tattaunawarsa da wani gidan radiyon Faransa ya ce dole ne kayyayakin agaji su shiga Gaza ba tare da wani sharadi ba don Isra'ila ba ta da hurumin da za ta ce ga wanda zai ci abinci ga kuma wanda ba zai sha ruwa ba.
Kazalika taron da ya hada da kungiyar kasashen musulmi, zai mayar da hankali wajen warware rikicin samar da yanci kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Bayan da Tarayyar Turai ta yanke shawarar sake duba yarjejeniyar hadin gwiwa da Isra'ila, Albares ya ce "dole ne su yi mai yiwuwa don dakatar da wannan yakin kuma a dauki matakin ladabtarwa ga Isra'ila".
Karin Bayani: Netanyahu ya zargi kawayensa da taimakon Hamas