Southampton ta sayi dan wasan Rangers
July 10, 2022Talla
Kungiyar kwallon kafar Southampton da ke gasar Firimiyar Ingila ta rattaba hannu kan kwantaragin shekaru hudu da dan wasan Najeriya Joe Aribo. Sanarwar da mahukuntan kulob din Southampton suka fitar a ranar Asabar ta ce sun cefano dan wasan tsakiyar ne daga kungiyar Rangers ta Scotland.
Kawo yanzu kungiyoyin kwallon kafa na Rangers da Southampton ba su bayyana kudin da aka yi ciniki dan wasan ba, amma wasu jaridu a Burtaniya na cewa kudaden su haura Dala 7,000.