Sonko ya jaddada bukatar hadin kai kan tsaro a Sahel
May 31, 2025Firaministan Senegal Ousmane Sonko ya jaddada wannan bukata ta hada kan kasashen Afirka don yakar ta'addanci, a lokacin da ya gana da shugaban kasar Cote d'Ivoire Alassane Ouatara a ziyarar da ya kai birnin Abidjan. Kasashen yankin Sahel da dama da suka hada da Mali da Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso na fama da munanen tashe-tashen hankula masu nasaba da kungiyoyin jihadi wadanda suka yi ajalin dubun-dubatar al'umma, lamarin da sannu a hankali ke yaduwa zuwa kasashen da ke gabar Teku.
Dama dai a tsakiyar wannan wata na Mayu da ke bankwana a yayin wata ziyara da ya kai Ouagadougou, Ousmane Sonko ya bayyana yuwuwar hada kai da gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso domin yakar jihar da ke nema zama genbo a yankin yammacin Afirka. Senegal dai na kokari taka rawa wajen shiga tsakanin kasashen kungiyar AES wato Mali da Nijar da Burkina da kungiyar ECOWAS wadda suka balle daga cikinta a watan Janairun da ya gabata.