An nada sabon firaministan Sudan
April 30, 2025Gwamnatin mulkin sojan kasar Sudan karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan a wannan Laraba ta nada Dafallah al-Haj Ali tsohon jami'in diflomasiyya na kasar a matsayin sabon firaminista, shekaru biyu bayan kasar ta fada cikin yakin basasa, tsakanin sojojin gwamnatin da bangaren rundunar mayar da martani ta RSF da Mohamed Hamdan Daglo yake jagoranci.
Karin Bayani: Mayakan RSF na ci gaba da halaka 'yan gudun hijira a lardin Darfur
Ambasada Dafallah al-Haj Ali ya shafe shekaru da dama yana aikin diflomasiyya inda ya kasance tsohon jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya lokacin mulkin tsohon Shugaba Omar al-Bashir kuma aiki na karshen da ya yi shi ne jakadan kasarsa a kasar Saudiyya.
Shi dai sabon Firamminista Dafallah al-Haj Ali ya maye gurbin Osman Hussein wanda yake rike da mukamun tun shekara ta 2021. Kana Janar Abdel Fattah al-Burhan ya nada Omar Sediq a matsayin ministan harkokin wajen kasar ta Sudan.