Sojojin Nijar sun hallaka a Côte d'Ivoire
June 9, 2012Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wasu ma'aikatan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya a Côte d'Ivoire inda suka hallaka mutane bakwai bayan da suka yi musu kwanton ɓauna. Bisa bayyanan mai magana da yawun twagar masu wanzar da zaman lafiyan, waɗannan ma'aikata 'yan asalin Nijar sun gamu da ajalinsu lokacin da suke sintiri kan iyakar Côte d'Ivoire da Liberiya.
Manzo na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya a wannan ƙasa da ke yammacin Afirka Mr Bert Koenders ya ce wannan rukunin masu wanzar da zaman lafiyan na daga cikin ƙarin dakarun da aka kawo kan iyakar domin inganta tsaron yankin a wani matakin da majalisar ta ɗauka kwanan nan dan rage yawan barazanar harin da fararen hulan kan iyakar ke fuskanta
Tuni dai babban sakataren Majalisar inkin Duniya Ban Ki- Moon ya yi kira ga mahukuntan Côte d'Ivoire da su ƙa´ddamar da binciken da zai gano musabbab in wannan ta'asa.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Yahouza Sadissou Madobi