Sojojin Nijar na amfani da Bazoum a matsayin garkuwa-Lauyoyi
July 25, 2025Lauyoyin sun bayyana hakan ne a daidai lokacin da Bazoum da mai dakinsa ke cika shekaru biyu a tsare a cikin wani yanayi na daurin talala a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, tawagar lauyoyin sun sanar da cewa sun yi duk mai yiwuwa wajen shigar da kararraki da kuma kiraye-kiraye na bukatar sakin Bazoum amma abin yaci tura.
Karin bayani:Ana kara neman ganin an sako Bazoum
Guda daga cikin lauyoyin 'dan asalin Amurka Reed Brody, ya ce a baya yana tattaunawa da Bazoum ta wayar tarho, amma tun daga watan Oktobar 2023 ya daina jin duriyar tsohon shugaban kasar, bayan an yanke musu duk wata sadarwa.
Karin bayani:Kungiyoyin kasa da kasa na neman a saki Bazoum
Mr. Brody ya sanar da cewa a bara sojojin sun saki 'dan Bazoum Saleem da mahaifiyarsa, amma ita taki amince wa da tayin sojojin inda ta bukaci kasance wa a tsare da mijinta. Lauyan na Amurka ya tabbatar da cewa Bazoum da shugaban gwamnatin mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani, na zaune a cikin fadar shugaban kasa, inda yake amfani da Mohamed Bazoum a matsayin garkuwa.