Sojojin Najeriya sun halaka 'yan bindiga 79
January 25, 2025Talla
Rundunar sojin Najeriya ta hallaka 'yan bindiga kusan 80 a cikin makon da ya gabata. ta sanar da haka ne a ranar Jumu'a, inda mai magana da yawunta Manjo Janar Edward Buba ya fitar da sanarwa yana mai cewa sabon samame da dakarunsu suka kadamar a sassan Najeriya dabam-dabam ya kai ga kama mutum 252 wadanda ake zargi da aikata munanan laifukada kuma kubutar da mutum 67 daga hannun masu garkuwa da mutane.
Cikin mutanen da aka kama akwai guda 28 da ake zargi da kwarewa wajen satar danyan man fetur a kudancin kasar, wanda ya dauki dogon lokaci yana haddasa wa Najeriya babbar asara a kudaden shigar da take samu.