Tashin farashin kaya a kasar Mali
February 28, 2025annan na zuwa ne a lokacin da gwamnatin mulkin sojin Mali ta kara kason kudi da take wa ware wa cibiyoyinta da kuma alawus da ta tanadar wa 'yan majalisar rikon kwarya, lamarin da ke girgiza wani bangare na al'ummar Mali. Fadar mulki ta Bamako ta bayyana cewar matsalar kamfar aljuhu ne ta sa ta kara haraji a kan wasu ababen more rayuwa irin su kira ta wayar salulu da sauransu. Ko da a taron majalisar ministoci da ta gudanar, sai dai gwamnatin mulkin sojin Mali ta ce neman warware matsalar makamashi musamman katsewar wutar lantarki ne ummal'aba'isan neman karin kudin shiga ruwa a jallo.
Karin Bayani: Mutum 48 sun mutu sakamakon ruftawar mahakar zinare a Mali
Youssouf Sissoko, dan jarida kuma daraktan yada labarai na jaridar l'Alternance, ya ce matakin da gwamnati ta dauka ba mummunan abu ba ne, amma dai ta yi kitso da kwarkwata saboda ba ta bi matakan fadakar da al'umma muhimmacin karin haraji ba, inda ya ce wayar da kai ya yi karanci musamman ma idan aka yi la'akari da cewa, akwai rashin amincewa ko yarda tsakanin masu mulki da talakawan da ake mula. Don haka, ya kamata hukumomi su ba da misali mai kyau don 'yan kasa su yi koyi da shi.
Sanarwar kari harajin na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi da cibiyoyin gwamnatin Mali daban-daban suka samu karin kaso a kasafin kudin gudanar da ayyukansu. Hasali ma dai, cibiyoyin da ke da kusanci da shugaban gwambatin mulkkin soja Janar Assimi Goita ne suka fi cin gajiya, lamarin da ke nuna irin son kai da na hannun daman shugaban ke nunawa.
Sékou Niamey Bathily, mai magana da yawun jam'iyyar Rassemblement pour le Mali ko Rally for Mali, ya ce gwamnati ta yi rabon dankali, inda ta fi dibar kaso mafi tsoka a matsayinta na hukuma ta kololuwa, duba da ma'aikatun da suka fi amfana da wannan da karin sabbin haraji da aka aza wa jama'a.
Sai dai jami'amn da suke dasawa da gwamnatin mulkin sojan Mali na neman wanke kansu daga zargin nuna son kai da ake musu. Kassim Keita, shugaban jam'iyyar APM kuma memba a majalisar rikon kwarya ta kasa, ya ce baikamata ma a bata lokaci wajen tafkan muhawarar kan matakin karin kasafin kudi ga hukumomin kasar ba, inda ya zargi 'yan Mali da kin biyan haraji domin ciyar da kasa gaba.
A wannan hali na kiki-kika game da yawan haraji a Mali, kowane mamba na majalisar dokokin rikon kwarya zai samu CFA miliyan biyu a kowane wata a matsayin albashi, yawan kudin da ke fusata akasarin al'ummar Mali.