Sojojin Kamaru 20 sun gamu da ajalinsu a harin Boko Haram
March 25, 2025Sojojin Kamaru 20 ne aka kashe a wannan Talatar, a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Wulgo na yankin Arewa maso gabashin Najeriya, a kusa da kan iyakar kasashen biyu. Wasu majiyoyi biyu d ke da kusanci da sojoji sun shaida wa kanfanin dillacin labaran AFP cewar, 'yan bindigan sun yi shiga tamkar makiyaya kafin su kutsa cikin garin tare da kai farmaki kan sansanin sojoji. Dama dai, dakarun Kamaru sun saba gudanar da ayyukansu akai-akai a yankin a matsayin wani bangare na yaki da masu ikirarin jihadi a kewayen tafkin Chadi sakamakon fama da fama da hare-haren Boko Haram da ISWAP.
Karin bayani: Ta ya za a magance shigar 'yan ta'adda Najeriya?
Tun bayan da mayakan Boko Haram suka yi asarar sansaninsu na Sambisa a 2021 ne, kungiyar ta koma yankunan da ke kusa da tafkin Chadi da suka hada da Wulgo, Waza, Gwoza, Pulka da tsaunin Mandara da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru. Tun daga shekarar 2009 ne, kalubalen tsaro a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya bazu zuwa kasashen Nijar da Kamaru da kuma Chadi da ke makwabtaka da kasar.