Sojojin hayan Rasha a Mali
January 7, 2022Manyan jami'an sojojin Mali sun tabbatar da cewa 'yan Rasha masu ba da shawara kan harkokin soja sun isa kasar da ke yankin yammacin Afirka, lamarin da ya janyo zaman tankiya da mayan kasashen Yammacin Duniya.
Wani jami'in soja da ya bukaci a sakaye sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa akwai kimanin 'yan Rashan 400 da ake sa ran za su isa kasar bisa manufofin yaki da tsageru masu dauke da makamai da ke tsananin kishin addinin Islama a kasar da ke yankin Sahel.
Kasashen Yammacin Duniya sun tir da matakin na amfani da sojojin haya na Rasha na kamfanin Wagner. Kasar Faransa wadda ta yi wa Mali mulkin mallaka ta turo sojoji domin yaki da tsagerun tun shekara ta 2013, kuma tana sahun gaba kan nuna takaicin gayyato sojojin haya daga Rasha zuwa kasar ta Mali, wadda yanzu haka sojojin ke rige da madafun iko.