Sojojin da ke biyayya ga Shugaba Kiir sun kama mataimakinsa
March 27, 2025Bangarori da dama a Sudan ta Kudu sun shiga zaman zullumi bayan da wasu sojoji dauke da manyan makamai suka kutsa kai a gidan mataimakin shugaban kasa Riek Machar tare da yin awon gaba da shi a babban birnin Juba. Kamun Riek Machar na zuwa ne bayan shafe tsawon wunin jiya ana ta harbe-harbe da manyan makamai a babban birnin Juba da jihar Planete mai fama da rikici, inda dakarun da ke biyeyya ga shugaban kasar Salva Kiir da na Riek Machar ke ta bata-kashi.
Yaki: Jamus za ta rufe ofishin jakadancinta a Sudan ta Kudu
Jam'iyyar Riek Machar ta yi Allah wadarai da kamun da jagoran nata, inda ta ce sai da aka kwance damarar dogaransa kafin daga bbisani a yi gaba da shi.Masu sharhi dai na ganin cewa M. Kiir mai shekaru 73 na kokarin tabbatar da magajinsa, tare da rage karfin fada ajin mataimakinsa kuma babban abokin hamyyarsa Riek Machar, lamarin da ya kara rura wutar rikicin.
Cafke ministan man fetur a Sudan ta Kudu
Tuni ofisoshin jadancin kasashen Jamus da Norway suka rufe, a yayin da Amurka ta bukaci 'yan kasarta da su fice daga Sudan ta Kudun bisa fargabar kara rincabewar rikici. Ko a kwanakin da suka gabata, wasu manyan kasashen duniya hudu da Kanada da Holkand da Kungiyar Tarayyar Turai sun yi kokarin sulhunta bangarorin biyu da ke gaba da juna, amma abin ya ci tura.