Sojoji takwas da Hamas ta sako sun isa gida Isra'ila
January 30, 2025Kungiyar Hamas ta Falasdinu na ci gaba da amfani da musayar fursunoni don isar da sako ga Isra'ila da duniya baki daya kan cewar har yanzu tana da karsashinta, duk da kashe jagororinta da wargaza dakarunta da Isra'ila ke tinkahon yi. Dubban dakarunta cikin cikakkiyar damara kuma kan sabbin motocin daukar sojoji sun gudanar da faretin nuna kwanji a yayin musayar fursunonin, wanda ya rikide zuwa ga bikin da dubban mazauna Zirin Gaza da Isra'ila ta nemi fattata daga zirin suka halarta, a farfajiyar gidan tsohon shugaban kungiyar da Isra,ila ke rike da gawarsa Yahya Sinwar.
Karin bayani: Farin cikin iyalai a Isra'ila da Falasdinu
Fursunonin da Hamas ta sako sun hada da mace daya Agam Berger da aka fito da ita daga baragujzan gine-ginen yankin Jabalaya sanye da warwaron tutar Falasdinu a hannunta. Su ma Arvel Yahud da Gady Moris an sako su, gami da wasu 'yan kasar Thailand biyar wadanda babu alamun wata wahalarwa ko fuskantar muzgunawa a fuskokinsu. Maimakon haka, dariya ba kakkautawa da daga hannun suka yi, da ke alamta samun nasara, tare da bayyana irin kyakkywan yanayi da mu'amallarsu ta kasance a yayin da ake tsare da su.
Isra'ila za ta ci gaba da auwatar da yarjejeniyar?
Dandazon jama'a da suka halarci taron sun ta shewa da fito, lamarin da ke nuna irin goyon bayan da kungiyar ta Hamas ke samu da tabatar da rashin dawowa daga rakiyarta da aka yi zaton mazauna Zirin na Gaza da suka dandana kudarsu na tsawon watanni 15 za su yi. Lamarin da ya sanya ministan tsaron cikin gidan Isra'ila Ben Gvir yin kira ga Natenyahu da ya janye daga karasa sauran matakan da suka rage na yarjejeniyar:
Ben Gvir ya ce: "A madadin dawo mana da wadanda ake garkuwa da su cikin wannan yanayin na cin fuska da wulakanci, gwanda mu kwaso gawawwakinsu da kanmu daga Gaza, bayan mun share ta daga doron kasa, an kuma daina jin duriyar Hamas baki daya.”
Karin bayani: Martani kan tsagaita wuta a yakin Gaza
A nata bangaren, Isra'ila ta fara sako wasu daga cikin fursunonin Falasdinawa 110 da ta yi alkawari, ciki har da gwamman wadanda ta yanke wa hukuncin daurin rai da rai, da mata 30 da yara kanana 30. Sai dai Isra'ilan ta yi kashedin daure duk iyalan da suka kuskura shirya bikin tarbar fursunoni, ko kuma sake kame shi kansa fursanan da ta sako.