Sojin Sudan sun kwace iko da fadar shugaban kasa na Khartoum
March 21, 2025Rundunar Sojin Sudan ta sanar da kwace iko da fadar shugaban kasa dake babban birnin kasar Khartoum a ranar Juma'a.
Wannan kwacen wata gagarumar nasara ce a yakin da sojojin suka kwashe shekara biyu suna bararraka wuta tsakaninsu da sojin kar ta kwana na RSF.
An kashe mutum tara a birnin El-Obeid na Sudan
To sai dai kuma bayan sanarwar sojin na Sudan da sa'o'i kalilan ita ma RSF ta ce tana nan a wajen fadar kuma ta kaddamar da farmakin da ya halaka gomman sojojin Sudan dake cikin fadar.
Majiyoyin sojin na Sudan sun ruwaito cewa mayakan RSF suna da nisan mita 400 kuma sun kai hari da ya kashe wasu sojoji tare da wani dan jaridan gidan talabijin na gwamnati guda daya.
Rikicin Sudan yana daukan hankali
Rundunar Sojin Sudan din dai ta dan samu koma baya na dan wani lokaci amma yanzu bisa la'akari da abinda ke aukuwa, ta dan fara farfadowa a fagen daga.