Gaza: Sojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa 14
July 30, 2025Yankin dai ya kwashe kusan watanni 22 ana gwabza yaki, kuma a halin yanzu, a cewar wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, mutane miliyan biyu na fuskantar matsalar yunwa.
Kakakin hukumar kare farar hula ta Gaza Mahmud Basal ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, mutane shida ne suka mutu sakamakon gobarar da Isra'ila ta tayar a kusa da wata cibiyar rarraba kayan agaji a yankin Arewa maso Yammacin garin Rafah da ke kudancin Gaza.
Wasu karin mutane biyu sun mutu wasu da dama kuma suka jikkata sakamakon wata gobarar da Isra'ila ta haddasa a lokacin da suke jiran agaji a kusa da mahadar Netzarim da ke kudancin birnin Gaza, da kuma wasu mutum biyu a wani hari ta sama da aka kai a kusa da Cocin Holy Family na birnin.
Ya kara da cewa an kashe wasu hudu a lokacin da suke jiran agaji a kusa da gadar Wadi da ke tsakiyar Gaza. Rundunar sojin Isra'ila ta shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa za ta binciki rahotannin.
Takunkumin kafofin yada labarai a Gaza da kuma matsalolin shiga yankuna da yawa na nufin AFP ba ta iya tantance adadin mutanen da hukumar da sauran bangarorin suka bayar ba.