Slovenia ta haramta wa ministocin Isra'ila shiga kasar
July 17, 2025Gwamnatin Slovenia ta sanar da cewa ta haramtawa Ministan Tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir da takwaransa na Kudi Bezalel Smotrich shiga kasar, sakamakon hannu da suke da shi dumu-dumu wajen keta hakkin bil Adama a kan Falasdinawan Zirin Gaza.
Karin bayani: Slovenia ta sanar da amincewa da Falasdinu a matsayin 'yantacciyar kasa
Ko a watan Yunin 2025, kasashen Kanada da Burtaniya da New Zealand da kuma Norway sun dauki makamanciyar wannan mataki na haramta wa Smotrich da Ben Gvir, da ke kasancewa kusoshin gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu shiga kasashen.
Karin bayani: Slovenia ta ƙarbi jagorancin Ƙungiyyar Eu
Ministar Harkokin Wajen Slovenia Tanja Fajon ta sanar da manema labarai cewa wannan shi ne karon farko da wata kasa a Turai ta dauki wannan mataki. Tun da fari dai, Shugabar kasar Slovenia Natasa Pirc Musar ta sanar da zauren majalisar dokokin EU cewa lokaci yayi da ya kamata a taka wa Isra'ila birki a kisan kiyashin da take yi a Gaza.